Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi matasa da ’yan kasuwa da ke siyarwa ko sayen kayan gwamnati da aka sace, musamman ƙarafunan fitilun titi, wayoyin lantarki da sauran kayayyakin da aka tanadar a tituna.
Wannan na cikin sanarwar da Khamis Bashir Bako Ayagi, mai ɗauko wa gwamna rahoto a Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano, ya fitar a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025 a Kano.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci ma’aikatar ayyuka ta tattaunawa da shugabannin masu sana’ar saye da sarrafa ƙarafa a jihar.
Haka kuma an kafa kwamitin da ya ƙunshi jami’an tsaro da sauran hukumomi domin dakile wannan matsala.
Gwamnatin ta jaddada cewa duk wanda aka kama da kayan gwamnati da aka sace, ko mai siyan su daga hannun barayi, za a ɗauki matakin doka a kansa.
Sanarwar ta kuma yi kira ga iyaye, shugabannin unguwanni da masu fada a ji su ja kunnen ’ya’yansu, tare da gargadin ’yan kasuwa da su guji siyan kayayyakin da aka sace daga wuraren gwamnati.