Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) kan yunƙurinta na kafa sabuwar majalisar dattawan Kano.
Gwamnatin ta bayyana cewa tun a Janairun 2024 gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa Majalisar Dattawan jihar ta Kano, wato (KEAC) wadda za ta riƙa ba da shawara kan ci gaban al’umma.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta ce “Tun bayan sanar da kafa wannan majalisar, ana ci gaba da shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da ingantaccen tsarin da zai ba da damar fara aiki yadda ya kamata.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “Wannan majalisar ba ta da wata alaƙa da siyasa ko jam’iyya, sai dai ta kasance dandalin bayar da shawara bisa hikima da gogewa.”
“Majalisar za ta ƙunshi fitattun mutane daga Kano ciki har da tsofaffin shugabanni, alƙalan kotuna, malamai, sarakuna, ƴan kasuwa da shugabannin tsaro,” kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Gwamnatin ta kuma bukaci dukkan ƙungiyoyi da mutane su haɗa kai da tsarin da aka kafa maimakon kirkirar wani abu sabo.
Wannan, a cewar ta, zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan majalisar da tabbatar da cimma burinta na kawo ci gaba da haɗin kai ga jama’ar Kano.
An ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a kammala tsarin kafa majalisar kafin gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da ita.