fidelitybank

Gwamnatin Kano ta bayar da wa’adin 31 ga wata kowa ya sabanta takardun filaye

Date:

Ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta kasa ta bayyana cewa a yanzu haka ta sake tantance filaye sama da 2000, tun bayan fara aikin a 2024 a matsayin wa’adin tabbatar da filaye na gwamnatin jihar Kano a ranar 31 ga Janairu, 2025.

Da yake bai wa manema labarai karin haske da safiyar Juma’a kan atisayen sake tantancewa, kwamishinan kasa da safayo da tsare-tsare na jihar, Mista Abduljabar Muhammad Umar, ya ce babu gudu babu ja da baya kan wa’adin.

Umar ya bayyana cewa, tun lokacin da aka fara tantancewar, ma’aikatar ta shaida sama da ayyuka miliyan daya na masu mallakar filaye da ke zuwa neman fom, rajista da sauran takardun tantancewa da ake bukata.

Ya yi gargadin cewa masu mallakar filaye da suka ki fitowa neman takardar shedar, suna fuskantar hadarin rasa filayensu a karshen atisayen a ranar 31 ga watan Janairu.

“Mun ba da dama don sake tantance sunayen filayen, wannan ya faru ne saboda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi imani da yin abubuwan da suka dace da bukatun jama’ar Kano kuma an ba da wa’adin don ba kowa damar sanin aikin.”

Umar ya bayyana cewa bayan kammala atisayen tantancewa a karshen watan Janairun 2025, ma’aikatar za ta fara ba da takardar shaidar gidaje da shaguna da filayen gona, inda ta nemi masu irin wadannan kadarorin da su dauki alfanun aikin domin kayansu.

Kwamishinan filaye, ya bada tabbacin cewa daga yanzu zuwa karshen wa’adin ma’aikatan ma’aikatar za su halarci duk wanda ya zo sabunta takardar mallakar fili.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp