Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa ta Barau FC da ta yi amfani da filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata, a matsayin filin wasa na wucin gadi a gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL) na kakar 2025 da 2026.
A cewar Mataimakin Daraktan Yada Labarai na kungiyar, Ashiru Gidan Tudu, an cimma wannan matsaya ne, bayan wata ganawar sirri tsakanin wakilan Hukumar Wasanni ta Jihar Kano da shugabannin Barau FC.
Asalin filin wasa na Barau FC, shi ne filin wasa na Dambatta da ke Kano ta Arewa, yanzu haka yana kan gyare-gyare a halin yanzu domin shiryawa sabuwar kakar wasa.
Da yake jawabi a yau Talata, Shugaban Barau FC, Ibrahim Shitu Chanji, ya tabbatar da cewa, Hukumar Wasanni ta Jihar Kano ta ba da izini ga kungiyar da su yi amfani da filin wasa na Sani Abacha tsawon kakar wasar gaba daya.
“Da farko, ina so in gode wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabiru Yusuf, bisa amincewa da bukatar mu ta buga wasanninmu a filin wasan Sani Abacha” inji Ibrahim Shitu Chanji’.
Ya kuma yaba wa Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso, bisa goyon baya da gudummawar da ya bayar.
Chanji ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su zama jakadu nagari tare da nuna hali na kirki a duk lokacin da suke halartar wasannin Barau FC a wannan kakar.
Barau FC zata karbi bakuncin Enyimba FC a wasan farko na gasar NPFL a ranar Lahadi, 24 ga Agusta, 2025, a filin wasan Sani Abacha, Kofar Mata, Kano.