Gwamnatin jihar Kano ta daukaka kara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke na cewa ta biya diyyar Naira biliyan 30 ga wasu ‘yan kasuwar da suka rusa shagunansu.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a Simon Anogede, a lokacin da ta ke yanke hukunci a shari’ar da kungiyar ‘yan kasuwa ta shigar, ta ce abin da gwamnati ta yi na zalunci ne da kuma saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Sai dai kotun ta bada diyyar Naira biliyan 30 ga ‘yan kasuwar, maimakon Naira biliyan 250 da suka nema daga gwamnati.
Alkalin ya bayar da umarnin a biya kudin nan take.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce, ta daukaka kara kan hukuncin da ta bayyana a matsayin rashin adalci.
Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa, kotu ba ta yi daidai ba wajen yanke hukunci ga kungiyar ‘yan kasuwa saboda dokar amfani da filaye ta fito karara kan matsayin filaye a kowace jiha.
Ya dage cewa kotu ba ta da hurumin ko da sauraren karar saboda gwamnati ce kadai ta mallaki fili kamar yadda dokar amfani da filaye ta tanada.