fidelitybank

Gwamnatin Kano ki duƙufa wajen sakawa mata aikin yi – NDE

Date:

Hukumar samar da aikin yi ta kasa (NDE) ta yi kira ga gwamnatin Kano da ta tallafawa mata a kokarinta na duba matsalar rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa da ke addabar jihar.

Ko’odinetan hukumar ta NDE na jiha, Inuwa Abdullahi Adamu ne ya yi wannan rokon a wajen bude taron koyar da kasuwanci na kwanaki 4 (BBT), a Kano.

Adamu ya ce, duk da cewa hukumar na da kyakkyawar alaka da gwamnatin jihar Kano, amma ana bukatar karin taimako daga gare ta domin magance matsalar rashin aikin yi.

Kodinetan ya bayyana cewa, manufar BBT ita ce karfafa wa masu cin gajiyar kwarin gwiwar shiga kananan sana’o’i.

Ya ce, mahalarta 30 da aka zabo daga kananan hukumomi 8 ne za su ci gajiyar shirin, wanda wani bangare ne na shirin bunkasa harkokin kasuwanci (EDS) da NDE ta bullo da shi don sanya matasa su dogara da kansu da kuma inganta zamantakewarsu.

“Muna da wani sashen da muke kira Small Scale Enterprise Department. Mun gudanar da tsare-tsare sama da 6 a wannan sashin, inda muka horar da matasa 308 marasa aikin yi. Muna da Sashen Sana’a wanda muka gudanar da tsare-tsare guda 6. A karkashin wannan tsari, mun horar da matasa 1998 marasa aikin yi.

“Muna kuma da Sashen inganta ayyukan yi a karkara. Mun gudanar da tsare-tsare guda 4 a karkashin wannan sashe mun horar da matasa 250 marasa aikin yi.

A nasa jawabin babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan harkokin kasuwanci da shiga tsakani, Baba Abdullahi ya yi alkawarin fadada adadin mahalarta taron a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

legit nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...

Daga yau wankin koda a Najeriya ya koma dubu 12 maimakon dubu 50 – Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da rage farashin...

An ceto Mutane 25 da syka kife a kwale-kwalen Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto sun ce, sun samu nasarar...

An fara duba rabon gyaran arzikin Najeriya

Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya...

Kwallaye 6 da aka zurawa Santos a raga ta sanya Neymar ya fashe da kuka

Ɗan wasan tawagar Brazil, Neymar ya fice daga cikin...

Hukumar Shari’a ta magantu kan sadakin dubu 20 da ya yamutsa hazo a Kano

Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ce ba a...

Cutar Mashako ta yi ajalin Yara hudu a Kano

Rahotanni na cewa cutar mashaƙo wadda aka fi sani...

Cin zaben da NNPP ta yi a Kano cuwa-cuwa ne – Ata

Ministan Jiha na Gidaje da Cigaban Birane, Rt Hon...

Mutane kusan 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale...
X whatsapp