Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya gana da shugabancin kungiyar yan kasuwar tsohuwar Fanteka da a baya-bayan nan ta fuskanci ibtila’in gobara da ta yi sanadiyyar salwantar dukiya mai yawa.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, gwamnan ya bai wa yan kasuwar tabbacin sake sauya fasalin kasuwar ta hanyar hadakar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
A cewar gwamnan, idan aka kammala gina sabuwar kasuwar, za ta zama cibiyar masu sa’anar hannu mafi girma a Najeriya.