Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe Otal din Holiday Conference da ke jihar, saboda ajiye wasu dilolin kwayoyi da kuma kasa biyan kudin hayar fili da ta kayyade na tsawon shekaru biyar.
Farfesa Kabir Mato, kwamishinan kasuwanci, kirkire-kirkire da fasaha ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Juma’a a Kaduna cewa otal din da aka rufe a ranar 15 ga watan Yuni ya zama wata cibiya ta cin zarafin jama’a.
Ya ce, matasa kan shiga otal din don saye da shan miyagun kwayoyi.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar hayar da mahukuntan otal din suka rattabawa hannu da gwamnatin jihar ita ce ta tafiyar da harkokin kasuwancin na tsawon shekaru 15 a kan yarjejeniyar da za ta kare a watan Fabrairun 2022.
Kwamishinan ya kara da cewa, otal din ya gaza biyan gwamnati komai tun shekarar 2017.