Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna (KADSEMA), ta yi gargaɗin mutanen da ke zama kusa da wuraren da za a iya fuskantar ambaliya da su tashi zuwa wurare marasa haɗari.
Wata sanarwa da babban sakataren hukumar Usman Mazadu ya fitar, ya ce kananan hukumomi bakwai na cikin haɗarin fuskantar ambaliya musamman ma al’ummomin da ke kusa da magudanan ruwa.
Hukumar ta bayyana cewa ya zama wajibi ta sanarwa al’ummomi yiwuwar samun ambaliyar sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a ranar Lahadi 19 ga watan Agusta da kuma Litinin 19 ga watan, wanda kuma ake ci gaba da tafkawa.
Ya ce mamakon ruwan sama da ake samu zai iya janyo tumbatsar koguna, musamman ma a wasu ƙananan hukumomi da ke kusa da su.
“Ya kamata waɗannan al’ummomi da ke cikin barazanar fuskantar ambaliya su kasance cikin shirin ko-ta-kwana sannan su tashi zuwa wurare marasa haɗari domin kare kansu,” in ji shi.
KADSEMA ta ce ƙananan hukumomi da ke cikin barazanar fuskantar ambaliyar sun haɗa da Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, karamar hukumar Chikun, karamar hukumar Igabi, Sanga, Kagarko da kuma karamar hukumar Jema’a.