Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana shirinta na sauya wa makarantu 359 matsuguni sanadiyyar ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa a jihar.
Lokacin da yake magana a wani taro na masu ruwa da tsaki, Gwamna Uba Sani wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar, ya ce ayyukan ƴan bindiga kamar satar ɗalibai a Kuriga da wasu makarantu da ke faɗin jihar na dagula al’amura a ɓangaren ilimi.
Ya ce a dalilin haka ne yanzu haka gwamnati ta fara shirin sauya wa makarantu 359 matsuguni zuwa wasu wuraren da babu matsalar tsaro.
Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da hare-hare na ƴanbindiga waɗanda ke kashewa tare kuma da satar mutane domin neman kuɗin fansa a arewa maso yammacin Najeriya.
Hari na baya-baya nan da ya ɗauki hankali shi ne wanda ƴan bindigar suka kai a ƙauyen Kuriga da ke cikin ƙaramar hukumar Chikun, inda suka sace ɗalibai da malaman makarantar.