fidelitybank

Gwamnatin Jigawa za ta sayi hannun jari a KEDCO

Date:

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1, domin samun kashi 10 cikin 100 na hannun jari a kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO).

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu Sagir Musa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar. Ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen siyan hannun jari 500,000 daga Future Energy Africa Limited, babban mai saka hannun jari na KEDCO, ta yadda za a kara mallakar jihar daga kashi 7.5 zuwa kashi 10 cikin dari.

A cewar Musa, zuba jarin ya yi daidai da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar da KEDCO da nufin inganta wutar lantarki a fadin jihar Jigawa.

“MoU ta mayar da hankali ne kan tabbatar da samar da wutar lantarki mai inganci ga biranen Tier 1 da kuma cimma nasarar samar da wutar lantarki a yankunan karkara a fadin jihar nan da shekarar 2028,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kwangilar samar da fitulun hasken rana na Naira miliyan 595 a yankunan karkara.

Za a gudanar da aikin ne a karkashin kulawar ma’aikatar wutar lantarki da makamashi.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp