Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da rage lokutan aiki da awanni biyu a cikin azumin watan Ramadan na shekarar 2023.
Shugaban ma’aikatan, Alhaji Hussaini Ali Kila ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Sanarwar ta ce, yanzu haka ma’aikatan jihar za su kai rahoto ofishin da karfe 9 na safe kuma za su rufe da karfe 3 na rana tsakanin Litinin zuwa Alhamis, maimakon karfe 5 na yamma.
“Yayin da ranar Juma’a, ma’aikata za su bayar da rahoto da karfe 9 na safe kuma za su rufe da karfe 1 na rana,” in ji shi.
Ya ce an yi hakan ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati damar yin shiri don hutun watan Ramadan da kuma samun karin lokacin gudanar da ayyukan ibada na watan Ramadan.