Gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci ga mabuƙata a faɗin jihar a wani mataki na rage wa al’ummar jihar raɗadin tsadar rayuwa da ake fama da shi.
Cikin wata sanarwar da Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Auwal D Sankara ya wallafava ashafinsa na Facebook, ya ce an ƙaddamar da rabon kayan abincin ne don tallafa wa al’umar jihar musamman a lokacin azumin watan Ramadan.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa da na masara da taliya. ”An zaɓo waɗannan kayayyakin abinci ne domin biyan buƙatun al’umarmu na abinci da kuma girmamasu a wannan lokacin azumi mai ƙaratowa”, in ji sanarwar.
Kwamishinan ya ce don tabbatar da ingancin rabon kayan masarufin, gwamnatin jihar ta bi hanyar da za a kai ɗauki ga gidaje 8,000 da ba su gaza mutum uku a kowane gida ba a kowace ƙaramar hukuma.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan jihar, Umar A. Namadi, ya ce gwamnati za ta samar da cibiyoyi biyu a kowace mazaɓa da za a riƙa ciyar da mutane a binci a lokacin azumin, don tallafa wa al’ummar jihar musamman a wanna lokaci na matsin rayuwa.
Tun dai bayan matakin cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya sanar cikin watan Mayun shekarar da ta gabata, gwamnatoci a matakai daban-daban suka sha alwashin ɓullo da matakan rage wa al’ummar raɗaɗin rayuwa da cire tallafin man ya jefa su.


 

 
 