Gwamnatin Jihar Enugu ta gargaɗi ƴan haramtacciyar ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) a kan yin ƙafar-ungulu ga jarrabawar kammala babbar sakandire (SSCE) da za a yi a gobe Alhamis.
A yau Laraba ne gwamnatin jihar ta fitar da gargaɗin bayan da haramtacciyar ƙungiyar ta IPOB, ta buƙaci jama’a da kada su fita, su zauna a gida, a gobe Alhamis 30 ga watan Mayu, 2024, domin tunawa da ƴan Biafra da suka mutu a lokacin yaƙin basasa na Najeriya.
A gobe Alhamis za a yi jarrabawar lissafi ne ta kammala babbar sakandire ta SSCE (Theory and Objectives)
A sanarwar da kwamishinan yada labarai na gwamnatin jihar ta Enugu ya fitar ya ce umarnin ƙungiyar ya saɓa da magabatansu suka yi yaƙi a kai.
Gwamnatin ta buƙaci ɗalibai da duk wadanda suke da hannu a jarrabawar da sauran masu harkokin kasuwanci da su fito su ci gaba da gudanar da harkokinsu, da cewa ta tanadi matakan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.