fidelitybank

Gwamnatin Buhari ‘yan bindiga sun kashe mutane 63,111 – Shehu Sani

Date:

Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya caccaki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya zargi gwamnatinsa da tabarbarewar tsaro da ba a taba ganin irinsa ba a gwamnatinsa.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a shafin sa na X ranar Lahadi.

Sani wanda ke wakiltar Kudancin Kaduna, ya zargi masu ruwa da tsaki na Arewa da yin shiru duk da yawan kashe-kashe da aka yi a lokacin gwamnatin Buhari.

Tsohon Sanatan ya ci gaba da cewa ’yan Arewa da suka samu muryarsu kwatsam sun yi shiru tsakanin 2015 zuwa 2023 saboda tsohon shugaban kasa dan Arewa ne.

Mai fafutukar ya ce adadin wadanda suka mutu a cikin shekaru takwas na gwamnatin Buhari ya kai 63,111.

Rubutun nasa ya kara da cewa, “Da yawa daga cikinsu sun yi shiru, sun kuma amince da zubar da jini da garkuwa da mutane a Arewa tsawon shekaru takwas.

“Sun kira mu da sunaye iri-iri a kokarinsu na kare gazawar. Sun yi biris da gawarwakin ’yan uwansu, sun fi sha’awar kare Shugabansu.

“Sun yi shiru lokacin da aka kashe mutane kusan 63,111; An yi garkuwa da su sau biyu, ciki har da dalibai 1,680.

“Sun rasa muryarsu saboda wanda ke shugabantar a lokacin dan uwansu ne. Sun sami muryarsu a yau saboda wanda ke kan kujerar yanzu ba dan uwansu ba ne.”

nigeria peace corps

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp