fidelitybank

Gwamnatin Borno ta haramta sayar da man fetur

Date:

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayar da umarnin haramta sayar da man fetur a karamar hukumar Bama na jihar, ciki har da garin Banki.

Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne ayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.

Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke na daƙile ayyukan ƴan ta-da ƙayar baya.

“Na bayar da umarnin haramta sayar da da man fetur a garuruwan Bama da Banki da kuma wasu sassa na karamar hukumar Bama nan take,” in ji gwamna Zulum.

Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana saɓa umarnin zai fuskanci hukunci mai tsanani.

“Babu wanda doka za ta kyale, sannan babu shafaffe da mai – za mu hukunta kowaye.

Gwamnan ya bai wa hukumomin tsaro damar kama duk wani gidan mai ko kuma mutum da ya take wannan umarnin.

Ya Æ™ara nanata zimmar da gwamnatinsa ke yi na dawo da zaman lafiya ma É—orewa a jihar, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba da haÉ—in-kai a yaÆ™i da Æ´an ta-da Æ™ayar baya da ake ci gaba da yi.

naija legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp