An kai ƙarar tsohon shugaban Amurka Donald Trump da ƴaƴansa uku kan zargin almundahana biyo bayan wani bincike da aka yi a New York cikin harkokin kasuwancin iyalan.
Binciken ya yi zargin cewa, kamfanin Trump ya aikata laifuka da dama na almundahana daga tsakanin shekarar 2011 da 2021.
Atoni Janar ta New York, Janar Letitia James, tana neman kotu ta dakatar da Mista Trump da ƴaƴansa daga shugabantar duk wasu harkokin kasuwanci a New York.
Kamfanin Trump ya yi watsi da zargin aikata ba daidai ba. In ji BBC.


