Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya koka kan yadda gwamnatin da ta shude ta ki biyan kudin jarrabawar daliban da suka kammala jarrabawar kammala sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC da National Examination Council, NECO na tsawon shekaru uku.
Lawal ya bayyana cews hukumar jarabawar biyu na bin gwamnati zunzurutun kudi har Naira biliyan 3.4 wanda ya ce ya jawo durkushewar fannin ilimi gaba daya a jihar.
Gwamna Lawal wanda ya yi magana ta bakin kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Hon. Mannir Mu’azu Haidara, ya bayyana cewa gwamnatin da ta shude ta na bin WAEC bashin Naira biliyan 1.8, yayin da ta ci NECO biliyan 1.6.
“Daliban da suka kammala karatunsu na sakandare ba su iya ci gaba da karatunsu ba saboda WAEC da NECO sun ki fitar da sakamakonsu na tsawon shekaru uku.
“Amma lokacin da gwamnati mai ci ta zo, ta kawar da basussukan tare da tabbatar wa hukumar jarrabawar biyan kudi cikin gaggawa,” inji shi.
Da yake jawabi, ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawal ta sake bude hukumar ciyar da makarantun jihar da aka rufe saboda ba za ta iya biyan ‘yan kwangilar da ke kai wa daliban kayan abinci ba.
A cewarsa, gwamnati mai ci ta gaji rugujewar tsarin mulki ne sakamakon durkushewar bangarorin ilimi, tsaro, tattalin arziki da dai sauransu.
A ci gaba da cewa, Haidara ya jaddada cewa, a lokacin da sabuwar gwamnati ta hau mulki, ta gaji ma’aikata da ‘yan fansho da ke bin bashin albashin watanni hudu, wanda ya ce gwamnatin Lawal ta wanke.


