fidelitybank

Gwamnatin APC ba ta damu da rayuwar ‘yan Najeriya ba – PDP

Date:

Jam’iyyar PDP a Najeriya ta zargi jam’iyyar APC mai mulkin kasar da nuna halin ko-in-kula game da matsalar tsaro da ta addabi kasar, lamarin da ta ce shi ne ya janwo mummunan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, abin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum takwas da jikkatar mutane da dama.

A wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, jami’iyar ta PDP ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira rikon-sakinar-kashin da gwamnatin APC ke yi wa harkar tsaro a kasar.

Babbar jam’iyyar adawar dai na shan zargin gwamnatin APC da gazawa, amma kuma galibi ta fi yin matsin lamba kan batun matsalar tsaron wacce ta bayyana ta rinjaye sauran matsalolin da ake fama da su a kasar.

Ta ce kalaman da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da kuma gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai suka yi game da matsalolin tsaron da cewa hakan ya tabbatar da cewa akwai hadin-baki tsakanin ‘yan ta’adda da gwamnatin APC.

“Ikirarin da gwamnan Kaduna Malam el-Rufai da kuma Ministan Sufuri Rotimi Amaechi suka yi game da batun hare-haren ‘yan bindigar ya tabbatar da zargin da jam’iyar PDP ke yi cewa gwamnatin APC ta san inda ‘yan ta’addar suke, kana ta san shirin da suke yi na tayar da zaune tsaye a kasar amma ta ki daukar matakai da gangan,” in ji sanarwar.

”Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ce wasu ministocin APC mai mulki sun yi kafar-angulu wa bukatun da ya gabatar a taron majalisar ministoci cewa a kafa na’urorin bincike don kauce wa hare-haren ta’addanci a kan titin jiragen kasa na Kaduna zuwa Abuja, ya kara tabbatar da zargin cewa gwamnatin ta APC na bai wa ‘yan ta’adda damar gudanar da ayyukan ta’addancinsu cikin sauki kasar,” a cewar PDP.

A wani jawabi da Gwamna Nasiru El- Rufai ya yi a bainar jama’a a baya bayan nan ne in ji jam’iyar ta PDP, shi da kan ya yi wa gwamnatin ta APC bankada, wanda ta ce shi ma yana ciki – ya ce: “Mun san inda sansanoninsu suke, mun san inda suke, jami’an tsaron farin-kaya na SSS na da lambobin wayarsu, suna sauraronsu kuma suna ba ni rahoto. iN JI bbc.

Kazalika PDP ta jaddada ikirarin Ministan Sufuri Ameachi inda yake cewa: “Muna sane da matsalolin da za su faru. Mun san cewa muna bukatar na’urorin zamani …. Na yi gargadin cewa za a tafka asarar rayuka kuma ga shi yanzu an rasa rayuka…A lokacin da ka tunkari gwamnati da gaskiyar niyya amma abokan aikinka suka rika taka maka birki, abin bakin-ciki ne.”

vanguard newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp