Magajin garin birnin Uvalde a jihar Texas ta Amurka ya ce, za a rushe makarantar nan da wani ɗan bindiga ya kashe yara 19 da malamai biyu a watan da ya wuce.
A cewar BBC, Don Mclaughlin, ya sanar da hakan ne a wani taron hukumar birnin, inda mazauna birnin ke bukatar amsa a kan harin da aka kai makarantar.
Tun da farko wani jami’i a hukumar da ke kula da tabbatar da tsaron al’umma a Texas,Kanal Steve McCraw, ya shaida wa mahalarta taron cewa akwai kwakkwarar shaidar da ke nuna cewa jami’an tsaron da suka je wajen harin makarantar ba su yi abin da ya dace ba.
“An shafe fiye da awa ɗaya kafin su shiga ajin da aka kashe mutanen,” in ji shi.