Toshon shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, zai je Georgia a ranar Alhamis domin gabatar da kansa a kan tuhume-tuhumen da ake masa na neman juya sakamako da kuma katsalanda a cikin harkokin zaben shugaban kasar da ya gabata.
Ana kyautata tsammanin idan ya je za a dauki hoton yatsunsa da shi kansa.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, tsohon shugaban na Amurka ya bayyana tuhumar da ake masa a matsayin bi ta da kullin siyasa.
Tun da farko alkalin da ya bayar da belin Mr Trump ya sanya masa ka’idoji a kan amfani da kafafen sada zumunta.
Trump dai ya musanta dukan zarge-zarge 13 da ake yi masa, ciki har da ƙin biyan haraji da bayar da bayanan ƙarya.


 

 
 