Gwamnatin jihar Adamawa ta haramta ayyukan kungiyar kwararrun mafarauta ta Nijeriya a fadin kananan hukumomi 21 na jihar.
Matakin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Humwashi Wonosikou, sakataren yada labaran gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri ya fitar a Yola.
A cewar sanarwar, Fintiri ya haramta kungiyar ne biyo bayan rahotannin cin zarafi da kuma barazanar tsaro daga mafarautan.
Fintiri ya ce”Abubuwan da suka faru kwanan nan a kananan hukumomin Demsa, Numan, Lamurde, Guyuk da Shelleng suka tilastawa gwamnatin daukar matakin gaggawan”. Inji Fintiri.