fidelitybank

Gwamnati za ta yi gwanjan rukunin Gidajen Emefiele

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce, za yi wa ƴan Najeriya gwanjon rukunin gidaje da ta ƙwace a Abuja a hannun tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

Bayanin haka ya fito ne lokacin da ministan ma’aikatar gidaje da raya birane Ahmed Dangiwa da kuma shugaban hukumar EFCC Olanipekun Olukoyede, suka jagoranci wata tawaga zuwa rukunin gidajen da aka ƙwace, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

EFCC ce ta ƙwace gidajen waɗanda ke alaƙa da Emefiele a watan Disamban 2024, inda aka miƙa su ga ma’aikatar bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar.

Lokacin ziyarar gani da idon, Dangiwa ya sanar da cewa ma’aikatar za ta fara aikin duba ingancin gidajen.

Ya ce bayan kammala duba su, za a samar da wani shafi wanda ƴan Najeriya za su shiga su nemi damar saya.

Ministan ya ƙara nanata zimmar gwamnatin tarayya wajen yin komai bisa gaskiya da adalci, inda ya yi kira ga jami’an gwamnati da su guji shiga abubuwan da ba su dace ba.

A watan Afrilun 2025 ne, wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da buƙatar tsohon gwamnan Babban Bankin na neman a dawo masa da rukunin gidajen da gwamnati ta ƙwace.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp