Gwamnatin tarayya za ta yi wa wasu Fursunoni afuwa, domin ta rage cunkuson da ake fuskanta a gidajen gyara halin ƙasar.
Domin tabbatar da hakan ne, gwamnatin ta kafa wani kwamiti a ranar Laraba, ƙarƙashin ministan shari’a, Lateef Fagbemi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sakataren gwamnatin tarayya na Najeriya George Akume, wanda ya jagoranci kafa kwamitin, ya ce sashe na 175 na kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shugaban ƙasa damar yin afuwa ga fursunoni.
Ko a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, an yi irin wannan afuwar, inda a watan Afrilun 2022 aka yi afuwa ga wasu fursunoni, ciki har da tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye da tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame.