Gwamnatin tarayya ta ce za ta sanya tsarin Almajiri a cikin shirin ciyar da dalibai na kasa baki daya.
Babbar mataimakiyar shugaban kasa ta musamman kan ciyar da makarantun gida na kasa, Dakta Yetunde Adeniji, ta bayyana hakan a lokacin da ta kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Jigawa.
Ta ce sun kai ziyarar ne domin sanar da Gwamnan shirin Gwamnatin Tarayya na fadada shirin ciyar da makarantun kasar zuwa makarantun Almajiri.
Ta ce Tinubu na da sha’awar ganin an samar da isasshen abinci ga ‘yan makaranta a fadin kasar nan.
Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya godewa hukumar SSA bisa wannan ziyara, sannan ya kuma godewa shugaba Tinubu kan yadda ya amince da ci gaba da gudanar da shirin, ya kuma kara da cewa shirin ciyar da daliban ya samu nasara da tasiri a jihar Jigawa.
“A Jigawa mun san fa’idar shirin, kuma muna da sha’awar ganin ya dawo,” inji shi.
Ya kuma bada tabbacin goyon bayan da suka dace domin samun nasarar shirin.


