Gwamnatin tarayya ta ce, za ta rinƙa kama ɗaiɗaiku da kamfanonin da ke yin canjin kuɗi ta haramtacciyar hanya da ma su yi mata zagon ƙasa.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’uma na Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka a wani taro da aka shirya kan sabbin hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu ya ɓullo da su.
Shugaban ƙasar dai ya fito da manufofin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da suka haɗa da cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta yi wa naira farashi.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan ya ce Babban Bankin Kasar yana iya ƙoƙarinsa wajen samar da hanyoyin wadata kasuwar canji da garin kudi, yana cewa masu zagon-ƙasa na ta yi wa shirin CBN ɗin ƙafar-ungulu.
“A matakin daidaita farashi CBN zai samar da wadatacciyar dala sannan ya fitar da sabbin hanyoyin hada-hadarta ga bankunan kasuwanci da kuma ‘yan kasuwar chanji,” in ji sanarwar.