Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da gwamnoni sun kafa kwamatoci kan satar ɗanyen mai da kuma na harkokin tattalin arziki.
An ɗauki matakin ne a taron majalisar tattalin arziki ta Najeriya karo na 138 wanda aka yi ta intanet ranar Alhamis.
A cewar sanarwar da mai taimaka wa mataimakin shugaban Najeriyar kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, kwamatocin za su kasance ƙarƙashin shugabancin gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdurrazak da takwaransa na jihar Imo, Hope Uzodinma.
Ya ce an yi taron ne bayan tattaunawar da aka yi game da matsalolin da suka shafi tattalin arziki da kuma nazari kan tsare-tsaren magance matsin tattalin arziki na gajere da dogon zango.
Kwamitin inganta tattalin arzikin yana da alhakin samar da tsarin kula da batun cire tallafin mai da bijiro da tsarin kare tattaunawar albashin ma’aikata da batun hauhawar farashin kayayyaki da sauran lamuran da suka danganci tattalin arziki.
Mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnan jihar Gombe mai wakiltar arewa maso gabas da gwamnan Legas mai wakiltar kudu maso yamma sai gwamnan Akwa Ibom mai wakiltar kudu maso kudu da gwamnan Anambra mai wakiltar kudu masu gabas da gwamnan Neja mai wakiltar arewa ta tsakiya da gwamnan Kaduna mai wakiltar arewa maso yamma.

A ɗaya ɓangaren, kwamitin da aka kafa wanda zai kula da ɗanyen mai da magance satar shi zai zama a ƙarƙashin jagorancin gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnan Ogun mai wakiltar Kudu ta yamma da gwamnan Plateau mai wakiltar arewa ta tsakiya sai gwamnan Rivers mai wakiltar kudu maso kudu da gwamnan Borno mai wakiltar arewa maso gabas sai gwamnan Jigawa mai wakiltar arewa maso yamma da gwamnan Abia mai wakiltar yankin kudu maso gabas sai ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare da ministan kuɗi da gwamnan babban bankin ƙasa sai shugaban kamfanin NNPCL da shugaban hukumar raya yankin Neja Delta, NDDC da manyan hafsoshin tsaro.


