fidelitybank

Gwamnati za ta kashe Naira biliyan 250 don yaƙar Talauci

Date:

Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan a yayin wani bayani da ya yi kan rahoton ci gaban da aka samu a shirin rage talaucin na ƙasa da ake kira NPRGS a gaban kwamitin da ya jagoranta a ranar Laraba.

Ayyuakan da aka tsara aiwatarwa a bana ƙarƙashin NPRGS sun haɗa da: “Gina gidaje dubu ɗari ga masu ƙaramin ƙarfi, wanda zai samar da ayyukan yi miliyan ɗaya na kai-tsaye ko a fakaice.

“Faɗaɗa samun makamashi ta hanyar samar da fitilun gefen titi 1,200 a yankunan karkara da kuma wasu ƙananan tashoshin wuta da za a riƙa amfani da su a gonaki ƙarƙashin shirin Solar Naija.

“Samar da ayyuka miliyan huɗu da ɗari biyar na kai-tsaye ko kuma a fakaice ta hanyar shirin gina hanyoyi a yankin karkara waɗanda za su haɗa kasuwannin ƙauye 750 a faɗin Najeriya.

“Samar da taimakon naira biliyan tara ga masu gonakin da ba su da karfi a lokacin daminar bana karkashin shirin samar da akin yi a bangaren noma.

“Fadada rajistar mutanen da ke samun tallafin rayuwa da karin sunayen magidanta miliyan uku.”

A lokacin gabatar da bayanin, Ministan kasafin kudi da tsare tsare, Clem Agba, ya ce mutum miliyan biyu ne suka amfana da shirin NPRGS kai-tsaye a 2022.

Rahotansa ya bayyana cewa manoma miliyan daya da dubu 600 ne suka mafana da shirin karkashin shirin habbaka noma.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriyan ya fitar a jiya, ya ce matasa 13,000 sun samu horo kan kere-kere da kuma sana’o’in hannu a jihohi 6 da suka hada da Legas da Ogun da Enugu da Gombe da Kaduna da Nasarawa, yayin da ake shirin samar da irin wannan tsari ga matasa 2,000 a jihar Edo.

Ya ce sama da ‘yan Najeriya 8,000 aka ɗauka aikin shimfiɗa tituna a yankin karkara ƙarƙashin shirin samar da hanyoyi a karkara, inda aka gina hanyoyi 40 cikin kauyuka 120 a faɗin Najeriya.

“A duka Najeriya mutum 1,818,782 ne suke cin gajiyar shirin NPRGS, kuma an ɗauki mutum 9,527 aiki ƙarƙashin aikin ya zuwa yanzu.”

vanguard new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...
X whatsapp