A ranar Talata ne gwamnatin tarayya za ta gurfanar da Tukur Mamu, dan kasar da aka kama saboda tattaunawa a madadin ‘yan ta’adda.
Mamu, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume 10 da suka shafi bayar da tallafin ta’addanci da sauransu, zai fuskanci mai shari’a Inyang Ekwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Ofishin ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) ne ke gudanar da shari’ar.
Darekta mai shigar da kara na kasa (DPP) na tarayya, M.B. Abubakar.
Mai shari’a Nkeonye Maha na FHC, a ranar 13 ga Satumba, 2022, ya amince da tsare Mamu a hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Mamu ya jagoranci tattaunawar da ‘yan ta’addan na sakin fasinjojin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da aka yi garkuwa da su a watan Maris din 2022.
A cikin wannan watan ne hukumar DSS ta kai farmaki gidan sa, inda aka gano kayayyakin sojoji da kudaden kasashen waje da dai sauransu. Za a gabatar da su a kotu a matsayin shaida.
A watan Satumba ne aka dawo da Mamu gida bayan an kama shi a Alkahira, babban birnin Masar, a kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.