Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta haɗa gwiwa da wasu kamfanoni domin gina titin jirgn ƙasa mai ɗankaren gudu da zai kai tsawon kilomita 4,000 a jihohi shida na ƙasar.
Kamfanin De-Sadel Nigeria Ltd. na Najeriya da kuma China Liancai Petroleum Investment Holdings Limited na ƙasar China ne za su yi aikin, kamar yadda ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ya bayyana ranar Talata.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa wani kwamati ya gabatar wa Mista Akume ranar Talata bayanin kuɗaɗen kusan dala biliyan 60 da aikin zai laƙume.
A cewar shugaban kamfamnin De-Sadel Nigeria Limited, Mr Samuel Uko, matakin farko na layin dogon zai haɗe jihohin Legas da Abuja da Kano da kuma Rivers, inda zai kai nisan aƙalla kilomita 1,600.
“Aikin zai kasance mataki-mataki. Da zarar mun kammala wani mataki ‘yan Najeriya za su fara amfana da jirgin kafin cikar wata 36 da aka ɗiba domin kammala aikin baki ɗaya,” in ji Mista Uko.
Sakataren gwamnati ya ce ofishinsa zai mayar da hankali wajen tsettsefe bayanan kuɗin da za a kashe kafin gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da umarnin fara aikin.