Gwamnatin tarayya ta ce, nan da ‘yan makonni kaɗan masu zuwa za ta fito da wani tsarin da zai samar da kimanin dala biliyan goma, da za a yi amfani da shi wajen farfaɗo da darajar naira da kuma sauke farashin kaya.
Gwamnatin ta ce, za ta samar da kuɗin ne ta hanyoyin shigo da masu saka jari daga ketare da kuma samarwa kamfanin mai na NNPCL wadatattun kuɗaɗen ketare.
Hakan dai zai sauƙaƙawa ƴan Najeriya sauki wajen rage wahalhalun da ƴan ƙasa ke fama a yanzu.


