fidelitybank

Gwamnati za ta fara yi wa Dabbobi allurar rigakafi cutar Anthrax

Date:

Gwamnatin tarayya na shirin yi wa dabbobi huji ko riga-kafin cutar Anthrax, bayan ɓullar cutar a wata gona da ke Suleja a jihar Neja.

Ma’aikatar noma ta ce, ta ɗauki matakan da suka dace don daƙile cutar da hana yaɗuwarta, kuma gonar da ake magana, wadda ake kiwon shanu da tumaki da Awaki, har ta ɗauki matakan keɓe ta tare da sa’ido a kan ta.

Tun a watan Yunin da ya wuce, gwmanatin Najeriyar ta ankarar da al`ummar ƙasar game da ɓullar cutar a ƙasashen Ghana da Burkina Faso da kuma Togo. Wannan ne ma ya sa mahukunta suka gargaɗi al`umma da suke dinga ɗaukar matakan kariya.

Wani kwararren likitan dabbobi a Najeriya, Dakta Abubakar Sulaiman, ya ce duk da cewa cutar ba ta da saurin yaɗuwa, amma bil`adama ma kan harbu da ita idan ya ci nama ko gogayya da jikin dabbar da ta harbu.

Ya ce, ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kariya daga cutar, ita ce yi wa dabbobi huji kamar yadda mahukunta suka yi aniya.

A ƴan makwannin da suka wuce ne aka samu labarin ɓullar cutar a ƙasashen Ghana da Burkina Faso da kuma Togo.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp