Hukumomi a kasar nan na cewa, sun soma wani yunƙuri na cire harajin VAT da kuma harajin shigo da kaya a kan magunguna da kuma na’urorin lafiya.
Sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiyar ƙasar ta fitar, ta ce a yanzu haka an kusan kammala tsarin da yadda shugaban ƙasa zai bayar da umarni a kai.
“Matakin zai tabbatar da cewa hukumar tara haraji ta Najeriya – FIRS da kuma hukumar kwastam sun aiwatar da umarnin na cire harajin VAT a kan magani da kuma na’urorin lafiya,” in ji sanarwar.
A tsakiyar wannan shekarar, ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya sanar da cewa shugaba Tinubu ya sanya hannu a kan dokar samar da magani da sirinji da sauran kayayyakin lafiya a ƙasar.