Ministan albarkatun kasa na Najeriya, Dr Dele Alake, ya ce a wannan shekarar ta 2024 gwamnatin kasar za ta karbe karin lasisin wasu masu hakar ma’adinai a kasar.
Alake ya bayyana hakan ne a sakon sa na sabuwar shekarar 2024 ga ‘yan kasar daga gidansa a jihar Lagos.
Kamfanin dillacin Najeriya NAN, ya rawaito gwamnatin Najeriyar ta sanar da yi wa lasin hakar ma’adinai 1,633 daga hannun wadanda ba su biya kudaden da ya kamata su biya gwamnati da suka hada da haraji ba a shekarar da 2023 da ta wuce.
Ministan ya kara da cewa gwamnatin Najeriyar ta na gayyatar masu zuba jari daga kasashen ketare a fannin hakar ma’adinan, dan haka zamanin kin biyan gwamnati hakkinta ya wuce.
Ana fama da matsalar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a Najeriyar, da masu lasin da ba sa biyan kudaden haraji a fannin hakar ma’adinan.