fidelitybank

Gwamnati tarayya ta miƙa cibiyar wutar ta Zungeru ga ƴan kasuwa

Date:

Gwamnatin tarayya ta miƙa ragamar harkokin cibiyar wutar lantarki na Zungeru zuwa ga wani kamfani mai zaman kansa na Penstock Limited.

An bayyana haka ne a taron farko na hukumar NCP da ke tantance kadarorin gwamnati da suka kamata a sayar a bana da aka yi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Ana sa rai matakin zai inganta harkar samar da wutar lantarki tare da bayar da gudummawa sosai ga biyan buƙatun ƴan ƙasa game da makamashi.

An cimma yarjejeniyar ranar 13 ga watan Disamban 2023 tsakanin hukumar kula da kadarorin gwamnati BPE da kamfanin na Penstock Limited.

Bayan amincewar hukumar NCP, kamfanin ya amince ya biya kashi hamsin cikin 100 na kuɗin soma aiki ranar 5 ga watan Janairu.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima wanda ya jagoranci taron ya bayyana ƙudurin gwamnatin tarayya na sake fasalta bankin tallafawa ayyukan noma domin haɓaka ɓangaren noma da samar da abinci a ƙasa.

Da yake magana a taron, Shettima ya bayyana irin rawar da bankin zai taka wajen samar da abinci a ƙasa inda ya yi magana kan rassan bankin da ke yankunan Najeriya.

nan news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp