Gwamnatin tarayya na zuba biliyoyin kudi, don kare al’umma daga yaki da talauci a Najeriya.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wajen bikin ranar yaki da kwadago ta duniya na shekarar 2022 a ranar Alhamis a Abuja.
Ngige ya bayyana biliyoyin da aka kashe kan shirye-shiryen zamantakewa a matsayin allurar rigakafin talauci sau uku.
Ministan ya ce, gwamnati na kula da ‘yan kasa duk da raguwar kudaden shiga da kasar ke samu.
Da yake lura da cewa talauci ne ke kara rura wutar bautar da kananan yara, ya bayyana kwarin gwiwar cewa kyawawan manufofi za su sauya yanayin.
“Yara suna cikin haɗari. Don haka ne gwamnati da kungiyar ILO da sauran masu ruwa da tsaki suka yi aiki tukuru,” NAN ta ruwaito.
Ngige ya ce, jam’iyyun na kokarin kawo karshen bautar da kananan yara bisa tsarin SDG 8.7, kuma matasan ma’aikata suna samun kariya kuma suna aiki a cikin yanayin tsaro.
Ya bayyana cewa, shirin ciyar da yara kanana na kasa (NCSFP) ya yi niyya wajen samun karuwar shiga makarantun yara.
Ngige ya kuma ce, manufar ta tabbatar da ciyar da yara da abinci mai gina jiki, yayin da manoma da ‘yan kasuwa da masu dafa abinci ke samun kudi.
Ministan ya kuma sanar da cewa ana magance matsalar talauci ta hanyar tsarin musayar kudi na sharadi, Trader Moni da N-power.