Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta bayyana rashin jin daɗinta kan abun da ta kira halin-ko-in-kula da gwamnatin ƙasar ta nuna kan buƙatunta.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Farfesa Abdulkadir Muhammad, ya ce ƙungiyar na jan hankalin gwamnati ne a yanzu gabannin ɗaukar mataki.
Ƙungiyar ta ce shekara ɗaya ke nan da ta shiga yarjejeniya da gwamnatin kan dalilan da suka kai malaan jami’oin ƙasar shiga yajin aiki, amma gwamnatin ba ta cika ko ɗaya daga cikin yarjejeniyoyin da suka kulla ba.
Inda ta koka cewa hatta albashin watan Janairu da ya wuce, gwamnatin ƙasar ta biya malaman ne da manhajar IPPIS, saɓanin cire su da ƙungiyar ta buƙaci a yi.
A baya dai ƙungiyar ta shiga wani dogon yajin aiki na wata da watanni, wanda bayan shiga tsakani aka samu maslaha ta janye yajin aikin bisa alkawarin biya musu bukatun.