fidelitybank

Gwamnati ta yi mana alƙawarin ƙarya na binne Mahaifin mu – Iyalan Mutumin da ya zana tutar Najeriya

Date:

Iyalan Taiwo Michael Akinkunmi, mutumin da ya zana tutar Najeriya, sun ce sun gaji da jiran jana’izar karramawar da aka yi musu alƙawari, shekara guda bayan rasuwarsa yana da shekaru 87.

A maimokon jiran jana’izar da aka yi musu alƙwari, iyalan sun ce za su binne Akinkunmi, wanda aka fi sani da “Mr. Flag” a wannan makon a jihar Oyo, inda ya ke zauna.

Duk da fatan jana’izar da jihar ta yi, ɗan Akinkunmi, Akinwumi Akinkunmi, ya bayyana cewa iyalan sun zaɓi su binne shi, tare da tallafin da gwamnatin jihar Oyo ta bayar.

“Dole ne mu yi masa jana’izar da ya dace,” Akinwumi ya shaida wa BBC Focus on Africa podcast.

Taiwo Akinkunmi, wanda ya zana tutar Najeriya kafin ƙasar ta samu ‘yancin kai a 1960, mutum ne mai tawali’u.

An haife shi ne a Jihar Ibadan kuma ya yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnati a ma’aikatar noma har zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekarar 1994.

Duk da irin gudunmawar da Akinkunmi ya bayar, har zuwa lokacin da Nijeriya ta cika shekaru 50 da samun ‘yancin kai, ba a san shi ba a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan Nijeriya 50.

Bayan rasuwarsa ne wani Sanata ya nemi ayi masa jana’izar karramawa a jihar wanda har yanzu, bayan shekara guda kenan, babu wani abu da ya gudana abin da ya saka danginsa yanke shawarar binne sa da tallafin da gwamnatin jihar Oyo ta samar.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp