fidelitybank

Gwamnati ta yi barazanar riƙe albashin Likitocin da su ka tsunduma yajin aiki

Date:

Ma’aikatar lafiya ta bayyana rashin jin daɗinta kan matakin da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya, NARD, ta ɗauka na fara yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai, duk da ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na magance matsalolinsu.

A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Ado Bako, ya fitar, ya ce gwamnatin ta sanar da aiwatar da dokar “ba aiki, babu albashi” na tsawon kwanakin yajin aikin, ma’ana gwamnati za ta riƙe albashin likitocin da ke yajin aiki har tsawon kwanakin da suka ɗauka suna yajin aikin, kamar yadda dokar ƙwadago ta tanada.

Bako ya jaddada cewa wannan matakin ba yana nufin yin watsi da halascin damuwar likitocin ba ne amma matakin na da nufin tabbatar da cewa muhimman ayyukan kiwon lafiya sun ci gaba da kasancewa ba tare da samun wata katsewa ba don amfanin jama’a.

Likitocin sun fara yajin aikin ne a ranar Litinin, domin matsa wa gwamnati lamba ta ceto abokiyar aikinsu, Dr Ganiyat Popoola da ke hannun masu garkuwa da mutane tun cikin watan Disambar shekarar da ta gabata.

Bako ya ƙara da cewa, ma’aikatar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro, sun dukufa wajen ganin an sako Dakta Popoola, kuma a halin da ake ciki, akwai tattaunawa mai ƙarfi da ake yi don ganin a kuɓutar da ita daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ma’aikatar ta buƙaci likitocin da su koma kan teburin tattaunawa, inda ta jaddada muhimmancin samar da haɗin kai da kuma dawwamammen mafita kan ƙalubalen da ke fuskantar fannin kiwon lafiya a Najeriya.

Sanarwar ta sake jaddada aniyar ma’aikatar na yin tattaunawa mai ma’ana tare da yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin cimma maslaha mai dorewa

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp