Gwamnatin tarayya ta rage kuɗin tallafin karatu ga ɗaliban ƙasar da ke karatu a ƙasashen waje.
Gwamnatin ta rage kuɗin tallafin daga dala 5,650 zuwa dala 4,370, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito tare da wallafa wata takarda daga ma’aikatar ilimi ta Najeriya.
Matakin ya shafi ɗaliban da ke karatu a ƙasashen Rasha da China da Hungary da wasu ƙasashen ƙetare waɗanda gwamnatin tarayya ke ɗaukar nauyin karatunsu.
Kuma a cewar rahotannin, gwamnati ta rage yawan kuɗaɗen ne saboda dalilai na matsalar tattalin arziki.
Gwamnatin Najeriya dai ta tura ƴan ƙasarta zuwa wasu ƙasashe karatu ƙarƙashin wata yarjejeniyar ilmi tsakaninta da ƙasashen na ƙetare.
Sai dai wasu daga cikin ɗaliban sun koka kan rashin biyansu kuɗin alawus na tsawon watanni.


