Tawagar ƴan wasan ƙwallon kwando mata ta Najeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon ƙwando ta mata ta Afirka.
Wasu cikin ƴan wasan Najeriya sanye da tufafi masu launin kore fari kore ,irin na tutar Najeriya
Tawagar ta D’Tigress ta samu gagarumar tarba daga masoya ƙwallon ƙwanda a Najeriya, lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na Abuja.
Ministar matan Najeriya da ta al’adu yayin da suke shirin sauka daga jirgin
Ministar Mata Iman Sulaiman Ibrahim da takwararta ta al’adu, Hannatu Musawa ne suka yi wa tagawar rakiya tun daga birnin Abidjan zuwa Abuja.
Iman Sulaiman Ibrahim da Hannatu musawa sanye da tufafi masu launin tutar Najeriya da wasu cikin ƴan wasan
A ranar Lahadi ne tawagar D’Tigress ta lashe gasar ƙwallon ƙwando ta tama ta Afirka, bayan doke Mali da ci 78-64.
Hannatu Musawa ke zantawa da manema labarai
Wannan ne karo na bakwai da tawagar Najeriya ta lashe kofin gasar a tarihi, wanda kuma shi ne na biyar a jere da ta ɗauka.