Gwmnatin tarayya ta amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan tasoshin jiragen ruwa.
Ministan sufuri na ƙasar Mu’azu Sambo ne ya bayyana haka a ƙarshen makon da muke ciki a lokacin da ya halarci bikin bayar da kyaututtuka da hukumar da shirya wa ma’aikatanta.
Mista Sambo ya yaba wa jagorancin hukumar game da ƙoƙarinta wajen jin daɗi da walwalar ma’aikata.
Haka kuma ministan ya jinjina wa Babban manajan hukumar bisa abin da ya kira ”ƙoƙarin” da ba a taɓa gani ba da hukumar ta yi wajen tara kuɗin shiga ga ƙasar.
Babban Manajan hukumar Bello-Koko ya gode wa gwamnatin tarayya dangane da ƙarin albashin da ta yiu wa ma’aikatan hukumar.