Gwamnatin tarayya ta sake tsawaita wa’adin aikin tantance shaidar rijista ta dan kasa (NIN) da kuma rijistar yin layukan wayoyi na (SIM) har tsawon tsawon watanni uku masu zuwa a nan gaba.
Gwamnatin ta sanar da hakan ne a hukumace cewa, ta tsayar da ranar Maris 31, 2022. A matsayin rana ta karshe na yin rijistar dukannin bangarotin biyu.
Matakin dai na zuwa ne tun bayan da hukumomi su ka bayar da sanarwar shigar da lambobin rijistar katin dan kasa NIN da kuma na layin rijistar waya na SIM, domin tattabar dukannin bayan masu amfani da waya a Najeriya, domin magance matsalar tsaro da a ke fuskanta.