Gwamnatin ta ƙaddamar da sayar da shinkafa ƴar gwamnati kilogram 50 kan farashin N40,000.
Amma gwamnatin ta ce sai wanda yake da lambar katin ɗan ƙasa za a sayar wa shinkafar, kamar yadda ministan noma Abubakar Kyari ya bayyana.
Sai dai a sanarwar da ministan noman ya wallafa a shafinsa na Twitter, bai bayyana cibiyoyin da ƴan Najeriya za su samu shinkafar ba ƴan gwamnati
Tun a watannin baya gwamnati ta ce za ta karya farashin shinkafa domin rage wa ƴan ƙasar raɗaɗi, tsadarta a kasuwa.
Gwamnatin ta ce ta tanadi shinkafa ton 30,000 wanda aka gyara da za ta sayar a farashi mai rahusa.