Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar kan Comfort Emmanson, fasinjar nan da ake zargi da tayar da hankali a cikin jirgin Ibom Air.
Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ne ya sanar da hakan a ranar Laraba bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar jiragen sama.
Ministan ya ce an yanke wannan hukunci ne bayan duba lamarin da jin kiraye-kirayen wasu manyan mutane, da kuma la’akari da nadamar da wadanda abin ya shafa suka nuna.
Kamfanin Ibom Air ya amince ya janye ƙorafinsa kan matar, wadda aka tsare kan lamarin da ya faru ranar 10 ga watan Agusta inda aka zarge ta marin ma’aikaciyar jirgin da kuma yin rikici da jami’an kula da filin jirgin sama.
“A lokacin da ‘yansanda suka ɗauki bayaninta a gaban lauyanta, ta nuna nadama sosai kan abin da ta aikata,” in ji ministan.
Bidiyon da ya naɗi tirka-tirkar ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda ‘yan Najeriya da dama suka dinga sukar jam’ian tsaron ƙasar da kuma kamfanin jirgin na Ibom Air game da yadda aka fitar da matar da ƙarfin tsiya daga cikinjirgi, lamarin da ya jawo aka yi mata tsirara.