Ma’aikatar mata ta ce, za ta hana dukannin otal-otal na ƙasar nan bai wa ‘yan mata masu ƙananan shekaru ɗakuna.
Ministar al’amuran mata ta ƙasa, Uju Kennedy-Ohaneye ce ta bayyana hakan, a lokacin da take jawabi a wajen wani taron buɗe horaswa da bayar da tallafi a Abuja.
Mrs Kennedy ta ce, matakin ya zama wajibi a yunƙurin da ma’aikatarta ke yi don magance matsalar safarar bil’adama a ƙasar.
Ministar na mayar da martani ne game da wata yarinya ‘yar Najeriya da aka kuɓutar a Ghana bayan da aka yi zargin an yi safararta zuwa ƙasar domin sana’ar karuwanci.
Ta ƙara da cewa hukumarta ta shirya tsaf! domin fara yaƙi da matsalolin safarar mutane daga gobe Litinin.
Haka kuma ministar ta umarci masu makarantu a faɗin ƙasar su ɗauki mataki kan cin zarafin da ake yi wa malamai da kuma ɗalibai da ake samu a wasu makarantun ƙasar.