Najeriya ta hana kamfanonin sufurin jiragen sama na ƙasashen waje taɓa kuɗaɗensu da suka kai dala miliyan 450, a cewar wani jami’in ƙungiyar sufurin jirage ta duniya.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, hukumomin Najeriya, ƙasar da ta fi saura girman tattalin arziki a Afirka, sun dakatar da fitar da kuɗaɗen ƙasar waje don sayo kaya da kuma na masu zuba jarin da ke son kai wa ƙasashensu na asali.
Gwamnati ta ɗauki matakin ne saboda ƙarancin kuɗaɗen ƙasar waje da ƙasar ke fuskanta, musamman na dalar Amurka.
Mataimakin shugaban ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta masu sufurin jiragen sama reshen Afirka da Gabas ta Tsakiya (IATA), Kamal Al Awadhi, ya ce suna yin tattaunawa da gwamnatin Najeriya “mai matuƙar wuya”. In ji BBC.
“Mun yi ta kawar da kai da fatan za a sasanta kuma hakan ba zai haifar wa ƙasar matsala ba,” kamar yadda ya faɗa wa manema labarai a birnin Doha na Qatar ranar Lahadi.
IATA ta ce ƙasashen Afirka sun riƙe wa mambobinta jumillar kuɗin da ya kai dala biliyan ɗaya, inda na Najeriya ya fi sauran yawa.