Gwamnati ta dakatar da Akanta Janar na ƙasa, Ahmed Idris daga aiki.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan, bayan hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama shi, bisa zarginsa da almundahana ta Naira biliyan 80.
Ministar kuɗi,Zainab Shamsuna Ahmed ce ta dakatar da shi,.kamar yadda mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan fasahar intarnet da kafofin sada zumunta, Tolu Ogunlesi ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Ya bayyana cewa dakatar da aka yi wa Ahmed Idris za ta bayar da dama a gudanar da bincike na ƙwarai kan irin zarge-zargen da ake yi masa