Hukumar da ke sa ido kan kafafen yaɗa lbarai ta ƙasa, NBC, ta ci tarar Trust Television Network (Trust TV) naira miliyan biyar, saboda labarin da suka wallafa kan hare-haren da ake kai wa a jihar Zamfara mai taken “Nigeria’s Banditry: The Inside Story”.
Wata sanarwa da kamfanin Media Trust ya fitar ta ce, hukumar a wata takarda dauke da sa hannun darakta janar dinta, Balarabe Shehu Illela, ta ce, ta ci tarar Trust TV ne saboda ta yaɗa rahoto na musamman da ya saba ka’idojin wasu sassan ayoyin dokar hukumar.
Sai dai kamfanin Media Trsut ya ce, “Yayin da muke ci gaba da nazari kan matakin hukumar da kuma duba zabukan da muke da su, muna sanar da cewa a matsayinmu na gidan talabijin, mun yi amannar cewa, muna aiki ne, domin al’umma ta hanyar karin haske kan batun garkuwa da mutane mai sarkakiya da kuma yadda yake shafar miliyoyin jama’ar kasarmu.”
Sanarwar ta kara da cewa, rahoton ya bi salsalar zaman dar-dar a tsakanin al’umma da kuma abubuwan da suka sanya rikicin da ya sa wasu ke daukar makamai da ke jefa mutane cikin gagarumin halin kaka-na-ka-yi.
Ta ce, rahoton ya fito da matsalolin rashin adalci da kabilanci da rashin iya gudanar da mulki wadanda su ne ke haddasa irin wannan rikici.
Kazalika ya bayar da shawara kan yadda za a magance matsalolin ta hanyar tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed, da Sanata Saidu Mohammed Dansadau, da Farfesa Abubakar Saddique na Jami’ar Ahmadu Bello, da sauransu.
A makon jiya ne gwamnatin Najeriya ta yi tur da matakin da BBC da kuma Trust TV suka dauka na yaɗa rahoton na musamman, tana mai cewa za ta dauki mataki a kansu.


