Dangane da matsalar sufuri da mazauna yankin Badau da ke karamar hukumar Bagwai ke fuskanta, gwamnatin jihar Kano ta kammala shirin bayar da gudunmowar jiragen ruwa guda uku ga mutanen da ke wurin.
Gwamnatin za a kuma ta raba daruruwan Riguna na ruwa ga al’umma don gujewa asarar rayuka da kayayyaki. Al’ummar da ke fadama sun kuma samu Jirgin ruwa daga Hukumar Kula da Ruwa ta Kasa (NIWA).
Mukaddashin gwamnan jihar, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana haka, a lokacin da yake kaddamar da jirgin ruwan fasinja mai daukar fasinjoji 18 da NIWA ta samar.
A cewarsa, jiragen ruwa guda uku da rigunan ruwa da za a ba da su, an yi su ne don fasinjoji, da kuma jigilar jirgin ruwa mai wucewa daga kauyen Badau zuwa wasu al’ummomi a cikin garin Bagwai.
Gawuna ya ce, “Gudunmawar jirgin ruwan ya nuna damuwar gwamnatin tarayya da hukumar NIWA da shirye-shiryen yaba kokarin gwamnatin jihar na kawo tallafi ga al’ummar karkara.
Ina kuma kara tabbatarwa hukumar NIWA kan kudurinmu na yin aiki tare, domin inganta harkokin sufurin ruwa a jihar Kano.”
A yayin da yake taya al’ummar garin Badau murnar samun tallafin Jirgin ruwan, ya kuma bukace su da su bi duk ka’idojin kiyaye lafiyar jirgin, domin gudun sake afkuwar hadurran jirgin.
Manajan yankin na NIWA, Malam Nasiru Maude, ya ce, bayar da gudunmowar jirgin ruwan fasinja mai daukar fasinjoji 18, yana kara tabbatar da aniyar hukumar na tabbatar da tsaron harkokin sufurin ruwa a kasar nan.
Ya kara da cewa “Wannan wani bangare ne na kokarinmu na tabbatar da kare rayuka a magudanan ruwa, al’ummar Badau da ku yi amfani da rigunan da suka dace, domin kare lafiyarku a lokacin da kuke cikin jirgin ruwa”.
Ya kuma yabawa gwamnatin jihar Kano bisa gaggawa da take yi a lokacin da ake cikin halin neman agaji a kan magudanan ruwa.
Taron ya samu halartar mamba mai wakiltar mazabar Shanono/Bagwai, Yusuf Ahmad Badau; Sarkin Bichi; Alhaji Nasir Ado Bayero; Kwamanda, Kwalejin Sojin Ruwa ta Najeriya, Commodore U.M Bugaje; Shugaban karamar hukumar Bagwai, Inuwa Zangina Dangada; da sauran Jami’an Jiha da manyan baki. A cewar Authority.